Chelsea ta dora Sarri a kan sikeli

Maurizio Sarri

Asalin hoton, Getty Images

Maurizio Sarri zai ci gaba da jan ragamar Chelsea, illa dai wasannin da zai buga a nan gaba ne zai yanke makomarsa a Stamford Bridge.

Roman Abramovich bai boye fushinsa kan doke Chelsea da Bournmouth ta yi, da kwallayen da Man City ta zura mata 6-0 da fitar da ita a FA Cup da Man United ta yi a ranar Litinin ba.

Sai dai wasu wasanni da Sarri zai ja ragamar Chelsea ne za su tabbatar da makomarsa ta ko zai ci gaba da zama a Stamford Bridge ko a sallame shi.

Chelsea za ta karbi bakuncin Malmo a ranar Alhamis wadda ta doke 2-1 a Europa League, sannan ta fafata da Man City a wasan karshe a Caraboa a Wembley a ranar Lahadi.

Sarri ya doke Pep Guardiola 2-0 a watan Disamba a gasar Premier, amma ya yi rashin nasara a wasa na biyu da ci 6-0 a Ettihad a watan Fabrairu.

Sai dai kuma kocin na Chelsea ya ce zai iya lashe kofin farko tare da kungiyar a ranar Lahadi, idan ya zo fafatawa da City a Wembley.

Chelsea za ta buga wani wasan hamayya da Tottenham a ranar 27 ga watan Fabrairu, kuma idan ta yi rashin nasara za ta kara nisa da matakin hudun farko a gasar Premier.

Kungiyar ta Stamford Bridge tana ta shida a kan teburin Premier da maki 50, iri daya da wanda Arsenal ke da shi ta biyar , yayin da United ke ta hudu da naki 51.