Lyon ta kware renon 'yan kwallo su yi fice a duniya

Lyon

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Lyon ta Faransa ta yi suna wajen renon matasan 'yan kwallo wadan da kan yi fice a duniya.

Lyon ta dade tana yaye 'yan wasan da take sayar da su ga wasu kungiyoyin da suke shahara a fagen kwallon kafa a duniya.

Idan ka kwatanta da Karim Benzema zuwa kan Juninho Pernambucano, sun taka-rawar gani a Faransa daga baya suka zama fitattun 'yan wasa.

Ga jerin 'yan wasa 10 da suka buga Lyon suka yi fice a kwallon kafa

Karim Benzema

Dan wasan Real Madrid shi ne na hudu a tarihin yawan cin kwallaye a gasar Champions League.

Kafin ya koma Spaniya da murza-leda ya buga wa Lyon wasa 148, ya ci kwallio 66 ya kuma taimaka aka zura 27 a raga.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Alexandre Lacazette

Dan kasar Faransa shi ne wanda kungiyar Lyon ta sayar mafi tsada a tarihi, inda ya koma Arsenal kan Yuro miliyan 53.

A Faransa ya ci kwallo 129, ya taimaka aka zura 43 a raga.

Michael Essien

Jose Mourinho ya jinjinawa Essien wajen kwarewa buga wasan tsakiya, hakan ne ya sa ya koma Chelsea kan Yuro miliyan 38.

Ya buga wa Lyon wasa 96 ya ci kwallo 13.

Mahamadou Diarra

Diarra da Essien sun taka rawar gani a wasan tsakiya a Lyon, hakan ne ya sa Real Madrid ta biya Yuro miliyan 26 na Diarra inda ya koma Spaniya da murza-leda.

Diarra ya buga wa kungiyar Faransa wasa 170 ya kuma ci kwallo 14.

Samuel Umtiti

Umtiti ya lashe kofin duniya a gasar matasa ta duniya ta 'yan shekara 20 a 2013 da kuma kofin duniya da Faransa ta lashe a Rasha a 2018.

Dan wasan ya koma Barcelona a 2016 kan Yuro miliyan 25, inda ya ci kwallo biyar a wasa 170 da ya buga wa Lyon.

Juninho Pernambucano

Pernambucano daya daga cikin 'yan wasan da ya kware wajen cin kwallo a bugun tazara, ya kuma koma Lyon kan Yuro miliyan 2.5 daga Vasco da Gama,

Dan wasan ya kuma biya kudinsa bayan da ya buga karawa 343 a Faransa ya ci kwallo 100 ya taimaka aka zura 62 a raga.

Sonny Anderson

Lyon ta sayi dan wasan dan kasar Brazil daga Barcelona kan Yuro miliyan 19 a shekarar 1999, inda ya buga mata wasa 159 ya kuma ci kwallo 92.

Miralem Pjanic

Dan wasan da ke taka-leda a Juventus, ya bar Lyon zuwa Roma kan Yuro miliyan 11, ya kuma ci wa Lyon kwallo 16 ya taimaka aka zura 21 a raga a karawa 121 da ya yi.

Edmilson

Ya buga wa Barcelona sama da wasa 100, bayan da ya koma Spaniya daga Lyon kan Yuro miliyan takwas.

Edmilson ya buga wa kungiyar Faransa wasa 155 ya ci kwallo biyar.

Ludovic Giuly

Giuly da Samuel Eto'o sun lashe kofin Zakarun Turai na Champions League a Barcelona a 2005/06 karkashin Frank Rijkaard.

Giully ya ci wa Lyon kwallo 31 a fafatawa 111, daga baya ya koma Monaco kan Yuro miliyan 8.5 a shekarar 1998.