Liverpool da Munich sun tashi wasa lami

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool da Bayern Munich sun tashi karawa babu ci a wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.

Liverpool ta samu damar zura kwallo har sau biyu a hare-hare 15 da ta kai har da wadda Sadio Mane ya buga ta yi waje.

Ita kuwa Bayern Munich wadda ta tsare gida, ita ce kan gaba a taka leda da kaso 51 cikin dari, kuma sau tara ta kai hari ko da yake ba su nufi raga ba kai tsaye.

Sai dai kuma alkalin wasa Gianluca Rocchi ya bai wa Jordan Henderson na Liverpool katin gargadi ya kuma bai wa dan kwallon Munich, Joshua Kimmich.

Bayaern Munic za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu ranar 13 ga watan Maris.

Daya karawar tsakanin Lyon da Barcelona ita ma 0-0 suka tashi.