'Makomar Ozil a Arsenal na hannunsa'

Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Arsenal, Unai Emery ya ce makomar Mesut Ozil na hannun dan kwallon a kokarin da dan wasan ke yi na dawo wa kan ganiyarsa.

Ozil mai shekara 30, shi ne dan kwallon da ake biya mafi tsada a Gunners, bayan da yake karbar fam 350,000 duk mako, amma wasa 13 ya buga a karawa 26 da aka yi a Premier.

Emery ya ce 'ya kamata dan wasan ya kara kwazo a wajen atisaye da filin wasa idan yana da koshin lafiya.'

Ozil ya buga wa Gunners karawa 216 tun komawar sa can da taka-leda daga Real Madrid, a matsayin wanda ta saya mafi tsada a tarihi kan fam miliyan 42 a shekarar 2013.

Sai dai wasa daya Ozil ya buga wa Arsenal tun bayan Kirsimeti, sakamakon rauni da wasu matsaloli da dan kwallon Jamus din ke fama da su.

A watan jiya ne Emery ya bayyana dalilin da bai sa Ozil a wasa a watan Disamba ba, har ma ya kara da cewar dan kwallon yana da makoma a Arsenal.