Juve ba ta ji da dadi ba a gidan Atletico

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Atletico Madrid ta yi nasarar doke Juventus da ci 2-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League wasan farko na zagaye na biyu da suka kara ranar Laraba.

Atletico wadda Diego Simeone ke jagoranta an hana ta fenariti da kwallon da Alvaro Morata ya ci, bayan da alkalin wasa ya tuntubi na'urar da take taimaka wa alkalin tamaula yanke hukunci.

Jose Maria Gimenez ne ya fara ci wa Atletico kwallo daga yadi na takwas, bayan da Morata ya sa wa kwallon kai ta bugi Mario Mandzukic.

Haka kuma kungiyar ta kara na biyu ta hannun Diego Godin, bayan da ya buga tamaula ta bugi jikin Cristiano Ronaldo ta fada raga.

Dan wasan Atletico, Diego Costa da Thomas Partey da na Juventus Alex Sandro ba za su buga karawa ta biyu da za a yi a Italiya a ranar 12 ga watan Maris ba, sakamakon katin gargadi da aka ba su.

Tara daga 'yan wasa 11 da suka fuskanci Juventus a ranar ta Laraba, sun buga wa Atletico wasan karshe a Champions League, hudu daga ciki sun buga karawar karshe a 2014 da ta 2016.