Real ta yi wasa biyar a waje ba a doke ta ba

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid za ta ziyarci Valencia a wasan mako na 25 a gasar cin kofin La Liga da za su fafata a ranar Lahadi.

Kawo yanzu Madrid ta yi wasa biyar a jere ta ci karawa hudu ta yi canjaras daya, tana kuma fatan dora wa kan wannan kokarin.

Real ta fara da doke Espanyol 4-2 a La Liga wasan mako na 21 da ta kai ziyara, da kuma cin Girona 3-1 a Copa del Rey da yin 1-1 a Camp Nou da Barcelona.

Sauran wasannin da ta yi nasara a waje sun hada da doke Atletico Madrid 3-1 a Wanda Metropolitano da yin nasara a kan Ajax da ci 2-1 a gasar Champions League.

Cikin wasanni biyar da ta buga a wajen, Karim Benzema ya ci kwallo biyar, ciki har da wadda ya zura a ragar Espanyol da Girona da wadda ya ci Ajax a gasar Champions League.