An ci tarar Jurgen Klopp fam 45,000

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar kocin Liverpool, Jurgen Klopp fam 45,000 kan kalaman da ya yi, sakamakon alkalancin da Kevin Friend ya gudanar a gasar Premier.

Klopp ya soki yadda Friend ya gudanar da alkalancin wasan da suka tashi 1-1 da West Ham United, inda ya ce kar bar kwallon da suka ci tun farko ya shafi kwazonsu a karawar.

Kocin ya ce 'Ya ji cewar kwallon da suka zura a raga satar gida ce. Ina da tabbacin cewar alkalin wasa ya san halattacciya ce'.

Hukumar ta tuhumi kocin da yin kalaman da suka shafi ingancin Alkalin wasan da zargin sa da yin fifi ko.

Sadio Mane ne ya fara ci wa Liverpool kwallo tun kan a je hutu, amma kuma James Milner ya yi satar gida a wasan da suka yi a ranar 4 ga watan Fabrairu.

West ham ta farke ta hannun Michail Antonio tun kan a je hutun rabin lokaci, sai dai Klopp ya kara da cewar tun daga nan ne Friend ya rike wasan sakamakon kuskuren da ya yi.