An haramta wa Chelsea sayen 'yan wasa

Bertrand Traore

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Traore ya ci kwallaye hudu a wasanni 16 da ya buga wa kungiyar Chelsea

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga sayen sabbin 'yan wasa saboda ta karya dokokin daukar matasan 'yan wasa da kulob din ya yi.

Hukumar ta ce an karya doka a kan sayen 'yan wasa 29 daga cikin 92 da kungiyar ta dauka.

Haramcin wanda zai kai har zuwa karshen watan Janairun 2020, ba zai hana Chelsea sayar da nata 'yan wasan ba.

Kuma ba zai shafi kungiyar mata ta kulob din da kuma ta kwallon kafar Futsal.

Sai dai kulob din ya ce zai daukaka kara kan hukuncin na Fifa.

An kuma ci tarar kungiyar fam 460,000, inda ita kuma hukumar kwallon kafar Ingila ta FA aka ci ta tarar fam £390,000.

Haramcin ya zo ne bayan wani bincike da Fifa ta yi a kan wasu matasan 'yan kwallo da Chelsea ta saya, har da tsohon dan wasan gabanta Bertrand Traore.

"Mun yi maraba da yadda Fifa ta ce ba a karya doka ba a kan 'yan wasa 63, amma ba mu ji dadi ba kan yadda ta ki yarda da matsayinmu a kan ragowar 'yan wasa 29", kulob din Chelsae ya bayyana.