Jurgen Klopp ya ce Ole Gunnar Solskjaer ya cancanci zama kocin United

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jurgen Klopp ya ce Solskjaer ya yi namijin kokari

Manajan Liverpool Jurgen Klopp ya ce babu wata tantama game da bai wa kocin rikon kwarya na Manchester United Ole Gunnar Solskjaer aikin horar da kungiyar na din-din-din.

A ranar Lahadi mai zuwa ne kungiyoyin biyu za su fafata a gasar Premier, karon farkon tun bayan da Solskjaer ya maye gurbin Jose Mourinho da kungiyar ta sallama a watan Disambar bara.

Kocin dan asalin kasar Norway ya yi nasara a wasa 11 daga cikin 13 da ya jagoranci kungiyar, yayin da ya yi rashin nasara sau daya a hannun Paris St-Germain a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Klopp ya ce "yana da kwarewa, don haka ya cancanci a ba shi aikin,"

Klopp wanda kungiyarsa za ta fara wasan na ranar Lahadi a matsayin ta biyu a kan tebur.

Kuma maki 14 tsakaninta da United wacce ke ta hudu a kan teburin ya ce "babu tantama zai zama manajan kungiyar a shakara mai zuwa "wannan a bayyane take".

Kungiyar ta United karkashin jagorancin Solskjaer ta samu nasarar shiga cikin kungiyoyi hudun farko, inda ta samu maki 25 daga wasanni tara tun bayan da aka nada shi a watan Disamba.

Tun da farko dai kungiyar ta hada maki 26 ne daga wasa 17 na farkon gasar da ta yi a karkashin jagorancin Mourinho - matsayi ma fi muni da ta fuskanta a wannan matakin tun shekarar 1990-91.