Guardiola na son United ta ci Liverpool

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Manchester City, Pep Guardiola na fatan Manchester City za ta doke Liverpool a wasan da za su buga a tsakaninsu a gasar cin kofin Premier a ranar Lahadi.

City wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana, za ta kara da Chelsea a wasan karshe a Caraboa Cup a Wembley a ranar Lahadi.

Cikin kofunan da take fatan lashewa bayan Caraboa ya hada da FA cup da na Premier da take na daya a teburi da na zakarun Turai da ta kai zagaye na biyu.

Chelsea ta yi nasara a kan City a Community Shield da ci 2-0 a bana da wata 2-0 a gasar Premier, sai dai kuma an ci kungiyar Stamford Bridge 6-0 a Etihad.

Liverpool za ta kara da Manchester United wadda ta doke ci 3-1 a wasan farko a Premier bana, kwana daya da wasan ne United ta sallami Jose Mourinho ta nada Ole Gunnar Solskjaer.

Man City tana ta daya a kan teburin Premier da maki 65, Liverpool ma 65 ne da ita a mataki na biyu, za ta koma na biyu idan ta yi nasara a kan United wadda take ta hudu a teburin.