Ko Solskjaer zai doke Liverpool?

United

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool za ta ziyarci Manchester United domin buga wasan Premier karawar mako na 27 da za su yi a Old Trafford a ranar Lahadi.

Liverpool wadda ta buga fafatawa 26 tana ta biyu a kan teburin Premier da maki 65, biye da Manchester City wadda take ta daya da maki iri daya da na Liverpool.

Liverpool ta yi nasarar doke Manchester United 3-1 a cikin watan Disamba, kwana daya tsakani kungiyar Old Trafford ta kori Jose Mourinho ta kuma nada Ole Gunnar Solskjaer.

Solskjaer ya ja ragamar United wasa 13, ya yi rashin nasara a karawa daya a hannun Paris St-Germain da tashi 2-2 a gasar Premier da Burnley.

Cikin wadan da ya ci har da Arsenal da Tottenham da kuma fitar da Chelsea a gasar FA Cup a ranar Litinin.

Sai dai kuma Jurgen Klopp ya ci karo da koma baya, inda ya yi kunnen doki da Leicester City da kuma West Ham United, daga baya ya yi nasara a kan Bournemouth da ci 3-0 a gasar ta Premier.

Haka kuma Liverpool ta tashi wasa babu ci da Bayern Munich a gasar cin kofin zakaraun Turai ta Champions League da suka kara a Anfield.

Liverpool za ta ziyarci Jamus a wasa na biyu a gasar Champions League a cikin watan Maris.