Man Utd ta rike Liverpool a Old Trafford

Manchester United da Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta sake dare wa kan teburin Premier duk da ta tashi babu ci tsakaninta da Manchester United a Old Trafford.

Sai dai Liverpool ta barar da babbar damar samun maki uku a gidan Manchester bayan manyan 'yan kasar United uku sun ji rauni.

Yanzu Liverpool na saman tebur ne da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City da ke matsayi na biyu.

Manchester United yanzu ta dawo matsayi na biyar yayin da Arsenal ta hauro matsayi na hudu bayan ta doke Southampton.

Wasa 11 ya rage a kammala Premier, kuma Liverpool da Manchester City da Tottenham na iya lashe kofin gasar.

Yadda aka yi fafatawar a Old Trafford.

Asalin hoton, Ronald Grant

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters