'Yan Barca da suka ragargaji Lyon 5-1

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Barcelona za ta karbi bakuncin Lyon a wasa na biyu zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da za su kara ranar Laraba a Camp Nou.

Kungiyoyin biyu sun fafata a wasan farko a gasar ranar 19 ga watan Fabrairu a Faransa inda suka tashi wasa babu ci.

Tuni kocin na Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 20 da za su buga masa karawar da za suyi a Spaniya

'Yan wasa 20 da za su fuskanci Lyon:

Ter Stegen da N. Semedo da Piqué da I. Rakitic da Sergio da Coutinho da Arthur da Suárez da kuma Lionel Messi.

Sauran sun hada da Dembélé da Cillessen da Malcom da Lenglet da Murillo da Jordi Alba da Prince da Roberto da Vidal da Umtiti da kuma Aleñá.

Sau bakwai kungiyoyin suka fafata a gasar cin kofin Zakarun Turai, inda Barcelona ta yi nasara a karawa hudu da canjaras uku.

Tarihin wasa tsakanin Barcelona da Lyon:

2018/2019

19 Fabrairu 2019 Champions League

Lyon 0 - 0 Barcelona

2008/2009

11 Maris 2009 Champions League

Barcelona 5 - 2 Lyon

24 Fabrairu 2009 Champions League

Lyon 1 - 1 Barcelona

2007/2008

27 Nuwamba 2007 Champiomns League

Lyon 2 - 2 Barcelona

19 Satumba 2007 Champions League

Barcelona 3 - 0 Lyon

2001/2002

23 Oktoba 2001 Champions League

Lyon 2 - 3 Barcelona

10 Oktoba 2001 Champions League

Barcelona 2 - 0 Lyon

Labarai masu alaka