Chelsea ta kai zagayen gaba a Europa

Giroud Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea ta yi nasarar doke Dynamo Kiev da ci 5-0 a wasa na biyu zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa da suka fafata a ranar Alhamis a Ukraine.

Olivier Giroud ne ya ci mata kwallo uku rigis kuma jumulla ya ci tara a gasar, yayin da Marcos Alonso da kuma Callum Hudson-Odoi kowanne ya ci daidai.

Chelsea wadda ta lashe kofin na Europa a 2038 ta yi nasarar cin kwallo 8-0 gida da waje, bayan da ta fara cin 3-0 a karawar farko a cikin watan Fabrairu a Stamford Bridge.

A ranar Juma'a za a raba jadawalin wasan daf da na kusa da na karshe a gasar ta Europa a Switzerland a kuma ranar za a hada da jadawalin Champions League.

A ranar Lahadi Chelsea wadda take ta shida a teburin Premier za ta ziyarci Everton a wasan mako na 31 da za su kece-raini a Goodison Park.

Labarai masu alaka