Arsenal ta kai bantenta a Europa

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal ta yi nasarar kai wa zagayen gaba a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa, bayan da ta doke Stade Rennes da ci 3-0 a wasa na biyu da suka fafata ranar Alhamis a Emirtaes.

Pierre Emerick Aubameyang ne ya ci wa Arsenal kwallo biyu, sannan Ainsley Maitland-Niles ya zura daya a raga, hakan na nufin Gunners ta ci kwallo 4-3 gida da waje kenan.

A karawar farko da suka yi a watan Fabrairu a Faransa, Stade Rennes ce ta doke Arsenal da ci 3-1.

A ranar Juma'a ne za a raba jadawalin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da ta Europa a Switzerland karawar daf da na kusa da na karshe.

Kungiyoyi hudu ne a Ingila suka kai zagayen quarter final da ya hada da Liverpool da Tottenham da Manchester City da kuma Manchester United.

Yayin da Arsenal da Chelsea za su wakilci Ingila a gasar Europa a wasan daf da na kusa da na karshen.

Labarai masu alaka