Ramos ya buga wa Real wasa 600

Sergio Ramos Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Asabar Real Madrid ta yi nasarar doke Celta Vigo da ci 2-0 a wasan mako na 28 a gasar La Liga da suka kara a Santiago Bernabeu.

Sai da aka koma zagaye na biyu ne Real ta fara cin kwallo ta hannun Isco, kuma saura mintu 13 a tashi daga karawar Gareth Bale ya ci na biyu.

Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya buga fafatawar da aka fara da shi har karshen gumurzun, kuma wasa na 600 kenan da ya yi wa kungiyar.

Ramos din na kaka ta 14 a Santiago Bernabeu, inda wasa hudu ne kacal ba a fara da shi ba a 600 da ya buga wa Real, ya kuma ci kofi 20 ciki har da na Zakarun Turai.

Mai tsaron bayan ya buga dukkan karawar da ya yi wa kungiyar a gasar cin kofin Zakarun Turai, inda ya yi wasa 119 daidai da wanda ya yi wa Madrid a kofin Zakatun nahiyoyin duniya da na European Super Cup.

Cikin fafatawa 600 da ya buga wa Real Madrid ya yi karawa 417 a gasar La Liga, inda aka yi nasara da shi a wasa 281 da canjaras 63 da shan kashi a wasa 73, ya kuma ci kwallo 59 a raga.

Real wadda take ta uku a kan teburin La Liga da maki 54, za ta karbi bakuncin Huesca a karawar mako na 29 a gasar La Liga ranar 31 ga watan Maris.

Wasu 'yan wasa da ke kan gaba a buga wa Real La Liga:

Raúl 550

Sanchís 523

Casillas 510

Santillana 461

Hierro is fifth 439

Labarai masu alaka