A karon farko an ci Juventus a Serie A

Juventus Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Genoa ta yi nasarar doke Juventus da ci 2-0 a wasan mako na 28 a gasar cin kofin Serie A da suka fafata a ranar Lahadi.

Genoa ta ci kwallon farko ta hannun Stefano Sturaro, sannan ta kara na biyu saura minti tara a tashi wasa ta hannun Goran Pandev.

Cristiano Ronaldo wanda ya ci wa Juventus kwallo uku rigis a gasar cin kofin Zakarun Turai da ta doke Atletico Madrid a tsakiyar mako, bai buga wasan na ranar Lahadi ba

Wannan ne karon farko da aka ci Juventus a gasar Serie ta bana, bayan buga wasa 28 ta yi nasara a 24 da canjaras uku.

Juventus wadda take ta daya a kan teburi ta bai wa Napoli ta biyu tazarar maki 18, duk da cewar a ranar ta Lahadi ne Napoli za ta fafata da Udinese.

Labarai masu alaka