Liverpool ta dare teburin Premier

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Liverpool ta hau kan teburin Premier bana, bayan da ta je ta yi nasara a kan Fulham da ci 2-1 a wasan mako na 31 da suka fafata ranar Lahadi.

Sadio Mane ya fara ci wa Liverpool kwallo a minti na 28 da fara tamaula, bayan da aka koma zagaye na biyu ne Fulham ta farke ta hannun Ryan Babel.

Sai dai kuma saura minti tara a tashi daga wasan ne Liverpool ta ci na biyu a bugun fenariti ta hannun James Milner.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hau kan teburin Premier da maki 76, bayan da ta buga wasan mako na 31 a gasar.

Manchester City tana da maki 74 a mataki na biyu da kwantan wasa daya, bayan da ta yi gasar FA ranar Asabar ta kuma doke Swansea da ci 3-2.

City za ta ziyarci Fulham ranar 30 ga watan Maris a wasan mako na 32 a gasar ta Premier, ita kuwa Liverpool za ta karbi bakuncin Tottenham ranar 31 ga watan nan.

Labarai masu alaka