Super Eagles ta doke tawagar Masar

Nigeria vs Egypt Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta yi nasara a kan ta Masar a wasan sada zumunta da ci 1-0 a karawar da suka yi ranar Talata.

Tawagogin biyu sun fafata ne a filin Stephen Keshi da ke Asaba, jihar Delta, Nigeria, inda Paul Onuachu ne ya ci wa Super Eagles kwallon minti daya da fara wasa.

A ranar Asabar Masar ta buga kunnen doki 1-1 da Niger a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Ita kuwa Najeriya doke Seychelles ta yi da ci 3-1 ranar Juma'a, kuma ita ce ta fara cin kwallo ta hannun Odion Ighalo a bugun fenatiti, sai dai kan aje hutu ne Seychelles ta farke ta hannun Roddy Melanie.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Super Eagles ta kara guda biyu a raga ta hannun Henry Onyekuru da kuma Moses Simon.

Najeriya ce ta ja ragamar rukuni na biyar da maki 13 ta kuma samu gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi tsakanin watan Yuni zuwa Yulin bana.

Super Eagles ba ta je gasar kofin Afirka da aka yi a 2015 ba a Equatorial Guinea, sannan ba ta samu zuwa na Gabon da aka yi a 2017 ba.

Masar ce za ta karbi bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka a 2019, bayan da hukumar kwallon kafar Afirka, CAF ta karbe izinin da ta bai wa Kamaru.

Nageria ta lashe kofin nahiyar Afirka karo uku, ita kuwa Masar sau bakwai ta dauka.

Labarai masu alaka