Cristiano Ronaldo zai yi jinya

Portugal Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasa Cristiano Ronaldo bai karasa karawar da tawagar kwallon kafa ta Portugal ta tashi 1-1 da ta Serbia ba a ranar Litinin.

Tawagogin sun buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2020, inda Ronaldo ya ji rauni a minti na 31 da fara tamaula.

Serbia ce ta fara cin kwallo a bugun fenariti ta hannun Dusan Tadic, daga baya mai masaukin baki, Portugal ta farke ta hannun Danilo Pereira.

Sai dai kawo yanzu Portugal da Juventus ba su fayyace girman raunin dan wasan da kwanakin da zai yi jinya ba.

Tawagar ta Portugal wadda ke rike da kofin nahiyar Turai, ta buga kunnen doki biyu a jere kenan, bayan wanda ta yi da Ukraine ranar Juma'a.

Kungiyar Ronaldo wato Juventus tana ta daya a kan teburin Serie A da tazarar maki 15, za kuma ta fafata da Ajax a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Juventus ce za ta fara ziyartar Ajax ranar 10 ga watan Afirilu, sannan su buga gumurzu na biyu ranar 16 ga watan Afirilu a birnin Turin, Italiya.

Labarai masu alaka