United za ta yi wasannin sada zumunta

United Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta tsara yin wasannin sada zumunta da zarar an kammala kakar tamaula ta bana, domin tunkarar ta badi.

Red Devils za ta fafata da Perth Glory da kuma Leeds a Australia cikin watan Yuli, sannan ta kara da Inter Milan a Singapore da kuma Tottenham a Shanghai duk dai a watan na Yulin.

Haka kuma United za ta buga da AC Milan a birnin Cardiff a watan Agusta.

United za ta kara da Inter Milan a babban filin wasa na Singapore ranar 20 ga watan Yuni, daga nan ta ziyarci Shanghai don fafatawa da Tottenham a Hongkou ranar 25 ga watan.

Haka kuma kungiyar ta Old Trafford za ta fuskanci AC Milan ranar 3 ga watan Agusta a filin wasa da ake kira Principality Stadium da ke birnin Cardiff.

Tun farko United ta sanar da wasan sada zumunta da za ta yi da Perth Glory a filin Optus ranar 13 ga watan Yuli, sannan kwanaki hudu tsakani ta kara da Leeds.

Babban jami'i mataimakin shugaban kungiyar United, Ed Woodward ya ce suna cike da murna da za su je China karo na 15, bayan da wannan ne dama ta uku da za su ziyarci Singapore.

Ya kuma kara da cewar wadan nan wasannin sada zumuntar za su taimakawa United shirin tunkarar kakar badi, sannan za su samu damar yin hulda da masu mara musu baya kai tsaye.

Labarai masu alaka