Zidane ya yi wa 'yan wasan Real maraba

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan wasan Real Madrid sun koma yin atisaye, domin shirin fuskantar Huesca a gasar La Liga wasan mako na 29 da za su fafata ranar Lahadi.

Zidane wanda ya ja ragamar atisaye a safiyar Laraba ya yi wa 'yan wasa lale marhabin da dawo wa daga buga wa tawagoginsu tamaula.

Cikin wadan da suka yi atisaye tare da sauran 'yan wasan sun hada da Courtois da Reguilon da Modric da Kroos da Ceballos da kuma Bale.

Su kuwa 'yan wasa da suka hada da Casemiro da Vallejo sun motsa jiki ne da kayan zamani a rufaffen dakin atisayen kungiyar.

A kakar bana da Huesca ta karbi bakuncin Madrid a wasan farko ranar Lahadi 9 da watan Disamba a gasar La Liga, Real ce ta yi nasara da ci 1-0, kuma Gareth Bale ne ya ci mata kwallon a minti na takwas da fara tamaula.

Real tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 54, Atletico Madrid ce ta biyu da maki 56, inda Barcelona ce ta daya da maki 66.

Wasannin mako na 29 a gasar La Liga

Ranar Juma'a 29 ga watan Maris

Girona da Athletic de Bilbao

Asabar 30 ga watan Maris

  • Getafe da CD Leganes
  • FC Barcelona da Espanyol
  • Celta de Vigo da Villarreal CF
  • Deportivo Alaves da Atletico Madrid

Lahadi 31 ga watan Maris

  • Levante da SD Eibar
  • Rayo Vallecano da Real Betis
  • Sevilla da Valencia
  • Real Valladolid da Real Sociedad
  • Real Madrid da Huesca

Labarai masu alaka