Juventus ta shiga International Champions Cup

Juventus FC Hakkin mallakar hoto Juventus FC

Juventus ta sanar cewar ta shiga International Champions Cup na bana da za a yi a Singapore da New York da kuma Turai.

Wannan yana daga cikin shirye-shiryen da kungiyar ke yi na shirin atisayen tunkarar gasar kwallon tamaula ta badi.

Juventus za ta fara zuwa Singapore domin yin wasa da Tottenham ranar 21 ga watan Yuni a katafaren filin wasan kasar.

Kwana uku tsakani ne Juventus za ta je China domin buga wasan hamayya da Inter Milan, daga nan ta koma Turai domin fafatawa da Atletico Madrid a birnin Stockholm na Sweden ranar 10 ga watan Agusta.

Juventus tana ta daya a teburin Serie A, bayan wasan mako na 28 a gasar, sannan ta kai matakin daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, inda za ta fafata da Ajax.

Ga wasannin da Juventus din za ta yi:

21 Juli: Juventus da Tottenham Hotspur a Singapore

24 Juli: Juventus da Inter a China

10 Agusta: Atletico Madrid da Juventus a Stockholm

Labarai masu alaka