Munich ta dauki Lucas Hernandez

Hernandez Hakkin mallakar hoto Getty Images

Bayern Munich ta dauki mai tsaron baya na kungiyar Atletico Madrid, Lucas Hernandez.

Dan kwallon mai shekara 23, zai koma Jamus da murza leda ranar 1 ga watan Yulin 2019, kan yarjejeniyar shekara biyar kan Yuro miliyan 80.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Faransa, wanda da shi aka ci kofin duniya a Rasha a 2018, shi ne na biyu da ya koma Bayern Munich tun bayan da Niko Kovac ya karbi aikin horar da kungiyar.

Hernandez zai taka-leda tare da dan wasan Faransa da shima ya lashe kofin duniya a Rasha, Benjamin Pavard wanda ya koma Allianz Arena daga VfB Stuttgart.

A karshen mako ne Freiburg za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan mako na 27 a gasar Bundesliga, inda Boruusia Dortmund za ta yi wa Wolfsburg masauki.

Zuwan Hernandez Bayern: Abubuwa hudu da ya kamata ku sani

 1. Bayaern Munich ta dade tana neman Hernandez, inda a baya Munich ta sanar da cewar tana son sayen dan kwallon.
 2. A watan Fabrairu shugaban Bayarn Munich, Uli Hoeness ya ce a shirye suke su biya kunshin yarjejeniyar Hernandez a Atletico Madrid.
 3. A watan Disamba Atletico ta fitar da wata sanarwar cewar bata sayar da Hernandez ga Munich kamar yadda ake ta rade-radi a lokacin.
 4. Hakan bai karya gwiwar Munich ba kan zawarcin dan kwallon, inda yanzu zai koma taka-leda a Jamus a badi.

Ga wasannin mako na 27 da za a buga a gasar ta Bundesliga.

 • Hoffenheim da Bayer Leverkusen
 • Borussia Dortmund da Wolfsburg
 • Nuremberg da FC Augsburg
 • Werder Bremen da FSV Mainz 05
 • SC Freiburg da Bayern Munich
 • Fortuna Düsseldorf da Borussia Monchengladbach
 • RB Leipzig da Hertha Berlin
 • Hannover 96 da Schalke 04
 • Eintracht Frankfurt da VfB Stuttgart