An bai wa Solskjaer aikin horas da United

United Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta nada Ole Gunnar Solskjaer a matsayin kocinta na din-din-din kan yarjejeniyar shekara uku.

A watan Disamba ne United ta bai wa Solskjaer aikin rikon kwarya, inda ya maye gurbin Jose Mourinho wanda ta sallama.

Solskjaer ya buga wa United kakar tamula 11, shi ne ya ci mata kwallon da ya bata damar lashe kofin Zakarun Turai a 1999 a wasan karshe.

Lokacin da Solskjaer ya karbi aikin rikon kwarya a Old Trafford, United tana ta shida a teburin Premier da tazarar maki 11 tsakaninta da 'yan hudun farko.

Image caption Solskaer ya ci wasa kaso 73.7 cikin dari a matsayin kocin United

Sai dai kawo yanzu wasa daya aka doke ta a Premier a hannun Arsenal a watan nan, kuma tazarar maki biyu ne tsakanita da Gunners wadda take ta hudu a teburin gasar bana.

Solskjaer ya zama mai horas da United na farko da ya ci wasa shida a jere a Premier, inda ya doke tarihin da Sir Matt Busby ya kafa.

Image caption United tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya

United ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai a karon farko tun 2014, bayan da ta fitar da Paris St Gearmain, za kuma ta kara da Barcelona.

Har yanzu mataimakin Solskjaer, Mike Phelan yana da kwantiragi a kungiyar Central Coast Mariners da ke Australia, amma ana sa ran zai ci gaba da aiki a Old Trafford.

Labarai masu alaka