Paul Onuachu ya ci wa Najeriya kwallo mafi sauri a tarihi

Paul Onuachu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paul Onuachu shi ne ya ci wa Super Eagles kwallo mafi sauri a tarihi

Paul Onuachu shi ne tauraron tawagar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya bayan da ya ci wa Najeriyar kwallo a babban wasansa na farko a tawagar cikin dakika 10 kacal da take wasan.

Kwallon da dan wasan mai shekara 24 ya ci, ita ce kwallo mafi sauri da tawagar Super Eagles ta taba ci wadda kuma ita ce tilon kwallon da ta doke kasar Masar a wasan sada zumunta da suka yi ranar Litinin.

Har wa yau, kwallon dai ita ce nasarar Super Eagles ta farko a kan kasar Masar a cikin shekara 29. Sannan kuma ta jawo kocin tawagar da 'yan jarida da abokan wasansa har ma da 'yan kallo suna ta sumbatu a kan dan wasan.

"Dan wasan ya buga wasa biyu ne kawai, saboda haka ina ganin akwai abin mamaki game da shi", in ji Gernot Rohr kocin Super Eagles.

Gernot Rohr ya kara da cewa "samuwar Onuachu ta kara mana kwari a gaba wajen kai hari".

Hukumar kwallon kafar Turai ta Uefa ta ce kwallon da Christian Benteke ya ci kasar Gibraltar ita ce mafi sauri a wasannin kasa da kasa. Ya ci kwallon ne dakika 8.1 bayan fara wasa.

Onuachu ya zura kwallon ne yayin da John Ogu ya taba masa ita, inda shi kuma ya zagaye mai tsaron baya da tabawarsa ta farko sannan kuma ya cinye Masar din da tabawarsa ta biyu.

"Na ji dadin cin wannan kwallo mai kyau irinta ta farko ga Najeriya, saidai wasa daya ne kawai", Onuachu ya shaida wa BBC.

Ya kara da cewa "a kashin gaskiya ni ma na yi mamakin yadda ta zo cikin sauri, amma kwallon kafa ce, saidai kawai na gode wa abokan wasana."

Duk da irin yabo da dan wasan yake samu daga ciki da wajen Najeriya, shi dai ya ce kawai yana kokarin samun gindin zama ne a tawagar.

"Burina shi ne in wakilci Najeriya a gasar cin kofin kasashen Afirka ta Nations Cup amma na san dole sai na yi aiki tukuru don samun gurbi", in ji Onuachu.

Labarai masu alaka