Kun san 'yan baya da aka saya mafiya tsada a duniya?

Bayern ta dauki Lucas Hernandez a matakin mai tsaron baya da ta saya mafi tsada a duniya daga Atletico Madrid.

Dan wasan tawagar Faransa ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, kuma shi ne na biyu mai tsaron raga da aka saya mafi tsada a tarihin kwallon kafa.

A watan Yulin 2019 Hernandez zai koma Jamus da murza-leda, bayan shekara 12 da ya yi a Atletico Madrid.

Cikin masu tsaron baya 12 da aka saya mafi tsada a duniya, Manchester City ce ta dauki biyar daga cikinsu.

Mohammed Abdu ya tattara hotunan masu tsaron bayan kwallon kafa su 12 da aka saya mafi tsada a duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

1. Virgil Van Dijk (Yuro miliyan 85)

Daga Southampton zuwa Liverpool (2017/18)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

2. Lucas Hernandez (Yuro miliyan 80)

Daga Atletico Madrid zuwa Bayern (2018/19)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

3. Laporte (Yuro miliyan 65)

Daga Athetico zuwa Manchester City (2017-18)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

4. Benjamin Mendy (Yuro miliyan 57)

Daga Monaco zuwa Manchester City (2017/18)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

5. Kyle Walker (Yuro miliyan 56,5)

Daga Tottenham zuwa Manchester City (2017/18)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

6. John Stones (Yuro miliyan 56)

Daga Everton zuwa Manchester City (2016/17)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

7. David Luiz (Yuro miliyan 49.5)

Daga Chelsea zuwa PSG (2014/15)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

8. Rio Ferdinand (Yuro miliyan 46)

Daga Leeds United zuwa Manchester United (2002/03)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

9. Lilian Thuram (Yuro miliyan 46)

Daga Parma zuwa Juventus (2001/02)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

10. Nicolas Otamendi (Yuro Miliyan 45)

Daga Valencia zuwa Manchester City (2015/16)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

11. Thiago Silva (Yuro miliyan 42)

Daga Milan zuwa PSG (2012/13)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

12. Leonardo Bonucci (Yuro miliyan 42)

Daga Juventus zuwa Milan (2017/18)

Labarai masu alaka