Messi da Suarez za su buga wasan Espanyol

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images

Koci Ernesto Valverde ya ce Lionel Messi da Luis Suarez za su buga karawar da Barcelona za ta yi da Espanyol a ranar Asabar a gasar cin kofin La Liga mako na 29.

A wasan na hamayya na farko da suka kara a gasar, Barcelona ce ta ci 4-0, kuma Lionel Messi ne ya ci kwallo biyu a fafatawar.

Sai dai kuma kyaftin din Argentina bai buga wa tawagar kwallon kafa ta Argentina wasan da ta yi da Morocco a makon nan sakamakon jinya, shi kuwa Suarez yana murmurewa.

An tambayi kocin ko 'yan wasan biyu za su iya taka-leda a ranar ta Asabar? sai ya ce ''Suna murmurewa yadda ya kamata, ina fatan su buga mana wasan na hamayya''.

Barcelona tana ta daya kan teburin La Liga da maki 10 tsakaninta da ta biyu Atletico Madrid.

Messi na Barcelona ne kan gaba da yawan cin kwallaye a gasar ta La Liga, inda yake da 29 a raga, sai abokin karawarsa Suarez mai guda 18.

Dan wasan kungiyar Sevilla, Yedder ya ci 16 a raga, yana mataki na uku sai Stuani na Girona mai 16, da dan kwallon Real Madrid Benzema wanda yake da 13 a matsayi na biyar.

Wasannin La Liga mako na 29 da za a buga:

  • Girona da Athletic Bilbao
  • Getafe da CD Leganes
  • FC Barcelona da Espanyol
  • Celta Vigo da Villarreal CF
  • Deportivo Alaves da Atletico Madrid
  • Levante da Eibar
  • Rayo Vallecano da Real Betis
  • Sevilla da Valencia
  • Real Valladolid da Real Sociedad
  • Real Madrid da Huesca

Labarai masu alaka