Sarri ya roki Hudson-Odai ya zauna a Chelsea

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images

Maurizio Sarri ya roki Callum Hudson-Odoi ya zama daya daga fitatcen dan wasan tamaula a nahiyar Turai, amma ya ci gaba da zama a Chelsea.

Tuni Hudson-Odai ya buga wa babbar tawagar kwallon kafar Ingila wasa tun kan ya kware a buga Premier, kuma Sarri ya ce yana fatan dan wasan zai yi zamansa a Stamford Bridge.

A karshen kakar 2020 ne yarjejeniyar dan wasan za ta kare a Chelsea, kuma a watan Janairu kungiyar taki sallama tayin fam miliyan 35 da Bayern Munich ta yi wa dan kwallon.

An fahimci cewar Chelsea na son tsawaita kwantiragin matashin dan kwallon a Stamford Bridge kan karshen kakar da ake buga wa.

An tambayi Sarrin ko zai dunga sa matashin dan kwallon a wasa idan ya zauna a Chelsea? Sai ya kara da cewar ''Tun da muna buga wasa takwas tsakanin kwana 28, ina da tabbaci zai buga mana tamaula''.

Chelsea za ta fafata da Cardiff City a gasar Premier mako na 32 a ranar Lahadi, bayan kammala wasannin kasa da kasa da aka yi, inda Hudson-Odai ya yi wa Ingila wasa biyu.

Labarai masu alaka