Zidane zai jagoranci Real Madrid wasa na 50 a Bernabeu

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

Zinedine Zidane ya koma aikin horas da Real Madrid a karo na biyu da kafar dama, bayan da ya doke Celta Vigo 2-0 a gasar La Liga karawar mako na 28 a ranar Lahadi.

A ranar Lahadi ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Huesca a gasar mako na 29 a gasar La Liga, kuma shi ne wasa na 50 da Zidane zai ja ragamar kungiyar a Santiago Bernabeu.

Cikin wasa 49 da ya ja ragamar Madrid a gida ya ci karawa 36 wato kaso 73.4 cikin dari, da canjaras takwas da rashin nasara a fafatawa biyar.

Wasan farko da Zidane ya yi a matsayin kocin Real a Santiago Bernabeu shi ne wanda ta doke Deportivo La Coruna 5-0 a ranar 9 ga watan Janairun 2016.

Kwallaye 145 aka ci a wasannin da Zidane ya ja ragama a Bernabeu, kuma sai da Real ta yi wasa 21 a gida ba a doke ta ba tsakanin Maris din 2016 zuwa Afirilun 2017.

Jumulla kocin ya ci kofi tara a Real da suka hada da Champions League uku da kofin zakarun nahiyoyin duniya biyu da European Super Cups biyu da LaLiga da kuma Spanish Super Cup.

Labarai masu alaka