Man City na shirin lashe kofi hudu a bana

Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan wasan Manchester City da dama sun kammala jinya sun koma atisaye a shirin da kungiyar ke yi na lashe kofi hudu a kakar bana.

City ta yi fama da 'yan kwallonta da suka yi jinya sai dai kawo yanzu Kevin De Bruyne da Benjamin Mendy da Fernandinho da kuma Vincent Kompany duk sun murmure.

Haka shima Nicolas Otamendi da kuma John Stones duk sun koma atisaye, in banda Fabian Delph da bai kammala jinya ba.

Hakan ne ya karawa kungiyar kwarin gwiwa a wasannin da za ta ci gaba da yi a karshen mako, inda za ta fafata da Fulham a gasar Premier a ranar Asabar.

Pep Guardiola ya ce 'yan wasa 21 daga 22 duk suna cikin koshin lafiya, kuma zai buga gasar Premier biyu sai FA Cup, sannan ya fafata a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Saura wasa tara a kammala gasar Premier shekarar nan, kuma City wadda take da kwantan wasa daya tana ta biyu biye da Liverpool da tazarar maki daya tsakanin.

A cikin watan Afirilu City za ta buga wasan daf da karshe a FA Cup da Brighton, sannan ta fafata da Tottenham gida da waje a gasar zakarun Turai karawar daf da na kusa da na karshe.

Tuni dai kungiyar ta Etihad ta lashe Caraboa na bana, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea a bugun fenariti.

Labarai masu alaka