Griezmann na kanfar cin kwallaye

Atletico Hakkin mallakar hoto Getty Images

Atletico Madrid ta taka rawar gani a ranar Asabar, bayan da ta je ta doke Deportivo Alaves 4-0 a gasar mako na 29 a wasannin cin kofin La Liga na Spaniya.

Sai dai kuma Antoine Griezmann baya cikin wadanda suka ci wa Atletico kwallayen, hasali ma karawa ta bakwai kenan bai ci wa kungiyar kwallo ba.

Rabon da Griezmann ya ci kwallo tun ranar 16 ga watan Fabrairu a karawar da Atletico ta doke Rayo Vallecano 1-0, kuma shi ne ya ci kwallon.

Tun daga lokacin bai ci kwallo a wasan da Atletico ta yi da Juventus gida da waje da wanda ta yi da Villarreal da Real Sociedad da Leganes da Athletic Club da kuma Alaves ba.

Ko a kakar bara Griezmann ya yi kamfar cin kwallaye a Spaniya tsakanin ranar 30 ga watan Satumbar 2017 zuwa 18 ga watan Nuwambar shekarar da ta gabata.

Kuma kungiyoyin da bai ci ba a lokacin sun hada da Leganes da Barcelona da Qarabag gida da waje da Celta Vigo da Villarreal da Deportivo La Coruna da kuma Real Madrid.

Atletico za ta buga wasan mako na 30 a gasar La Liga da Girona ranar Talata, inda Griezmann ke fatan kungiyarsa ta yi nasara sannan ya kawo kanfar cin kwallaye da yake fama kawo yanzu.

Labarai masu alaka