'Yan Madrid da suka kara da Huesca

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid za ta karbi bakuncin Huesca a wasan mako na 29 a gasar cin kofin La Liga da za su fafata a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Wannan ne wasa na biyu da Zinadine Zidane zai ja ragamar Real a karo na biyu da ya koma horas da kungiyar, ya kuma bayyana 'yan wasa 19 da za su fuskanci Hueca.

Kuma wannan ne wasa na 50 da Zidane zai ja ragamar Madrid a Santiago Bernabeu, bayan da ya ci karawa 36 wato kaso 73.4 cikin dari, da canjaras takwas da rashin nasara a fafatawa biyar.

Real Madrid tana ta uku a kan teburin La Liga da maki 54, biye da Atletico Madrid ta biyu mai maki 59 da Barcelona wadda take ta daya da maki 69.

A kakar bana ne aka fitar da Real a Copa del Rey da gasar zakarun Turai ta Champions League.

Wadan da za su buga karawa da Huesca:

Masu tsaron raga: Navas da Luca da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Vallejo da Ramos da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Reguilon.

Masu buga tsakiya: Casemiro da Valverde da Llorente da Brahim da Isco da kuma Ceballos.

Masu cin kwallaye: Mariano da Benzema da Bale da kuma Lucas Vazquez.

Labarai masu alaka