Da kyar da gumin goshi Chelsea ta ci Cardiff

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea ta hada maki uku rigis ranar Lahadi, bayan da ta je ta doke Cardiff City 2-1 a wasan mako na 32 a gasar cin kofin Premier da suka fafata a Cardiff Stadium.

Cardiff ce ta fara cin kwallo ta hannun Victor Camarasa, saura minti biyar a tashi daga wasan ne Chelsea ta farke ta hannun Cesar Azpilicueta.

Kuma daf da za a tashi daga karawar Chelsea ta kara na biyu ta hannun Ruben Loftus-Cheek.

Da wannan sakamakon Chelsea tana nan a matakinta na biyar a kan teburi da maki 60 daidai da wanda Arsenal take da shi wadda za ta fafata da Newcastle United ranar Litinin.

Cardiff City tana ta 18 a kasan teburin Premier da maki 18 da tazarar maki daya tsakaninta da Fulham ta 11 sannan maki biyar tsakaninta da Burnley ta 17 a teburi.

Chelsea za ta buga kwantan wasanta da Brighton & Hove Albion ranar 3 ga watan Afirilu, karawar da ya kamata su yi tun 24 ga watan Fabrairu gasar mako na 27 a wasannin Premier.

Wasannin mako na 33 da za a buga:

Talata 2 Afirilu 2019

  • Watfordda Fulham FC
  • Wolverhampton Wanderers da Manchester United

Laraba 3 Afirilu 2019

  • Manchester City da Cardiff City
  • Tottenham da Crystal Palace Kwantan wasan mako na 31

Juma'a 5 Afirilu 2019

  • Southampton da Liverpool

Asabar 6 Afirilu 2019

  • Newcastle United da Crystal Palace FC
  • Huddersfield Town da Leicester City
  • Bournemouth da Burnley FC

Lahadi 7 Afirilu 2019

  • Everton da Arsenal FC

Labarai masu alaka