Heartland ta ci Kano Pillars

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Malikawa

Heartland ta yi nasarar doke Kano Pillars da ci 2-1 a wasan mako na 13 a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya da suka fafata ranar Lahadi.

Heartland ta ci kwallo ne ta hannun Godwin Okoko Emmanuel minti 12 da fara wasa, sai dai a minti na 22 ne Pillars ta farke ta hannun Rabi'u Ali.

Heartland ta yi nasarar cin kwallo na biyu ne bayan da Pillars ta ci gida ta hannun mai tsaron ragarta Ibrahim Idrissu, kuma hakan ne ya sa ta hada maki uku rigis a karawar.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi:

  • El-Kanemi 4-1 Akwa Utd
  • Sunshine Stars 1-0 Kwara Utd
  • Tornadoes 0-0 Rangers
  • Gombe Utd 1-0 Yobe Stars
  • Abia Warriors 0-1 Nasarawa Utd
  • Remo Stars 0-1 Rivers Utd
  • FC Ifeanyiubah 1-0 Plateau Utd
  • Bendel Insurance 2-0 Wikki

Labarai masu alaka