'Yan Man United nawa ne ke jinya?

United Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Asabar Manchester United za ta karbi bakuncin West Ham United a wasan mako na 34 a gasar cin kofin Premier da za su kara a Old Trafford.

Kocin United Ole Gunnar Solkjaer ya bayyana 'yan wasan da ke jinya da wadan da aka dakatar da buga tamaula sakamakon laifin da suka yi ya yi wasa.

A ranar 12 ga watan Afirilu Solskjaer ya ce Alexis Sansez ya fara atisaye, ana kuma kula da murmurwar da yake yi.

Rabon da dan kwallon tawagara Chile ya buga wa United tamaula tun farkon watan Maris a karawar da United ta yi nasarar doke Southampton 3-2 a gasar Premier.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ander Herrera da kuma Nemanja Matic ba su buga wa United karawar da ta yi da Wolves a gasar Premier da Barcelona a Champions League ba.

Rabon da 'yan kwallon masu buga wa United tsakiya tun fafatawar da ta yi da Watford a karshen watan Maris.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Eric Bailly ya yi rauni ne a lokacin da yake buga wa tawagar kwallon kafar Ivory Coast tamaula, sai dai ya yi zaman benci a wasan da Arsenal ta ci United a gasar Premier.

Rabon da mai tsaron bayan ya buga wa Red Devils kwallo tun wasan zagaye na biyu da United ta yi da Paris St Germain a Champions League a Faransa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Matteo Darmian da kuma Antonio Valencia, rabon da Darmain ya buga wa United tun sauyi dan wasa da yi a fafatawar da United ta doke Brighton 2-1 ranar 19 ga watan Janairu.

Shi kuwa Valencia rabon da ya yi wa United tamaula tun 2 ga watan Janairu a karawar da kungiyar Old Trafford ta yi nasara a kan Newcastle da ci 2-0.

Wadan da aka dakatar

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ashley Young da Luke Shaw ba za su buga wa United karawar da za ta karbi bakuncin West Ham ranar Asabar ba.

Young ya karbi katin gargadi na biyu a fafatawa da Wolverhampton a wasan Premier, ba zai buga wasa daya ba.

Shi kuwa Shaw ba zai buga wasan da United za ta yi da Evrton ba ranar 21 ga watan Afirilu, bayan da mai tsaron bayan ya karbi katin gargadi 10 jumulla.

Haka kuma a gasar cin kofin Champions League, Luke ba zai buga karawar daf da na kusa da na karshe da United za ta ziyar ci Barcelona ba.

Labarai masu alaka