Man United ta koma ta biyar a teburin Premier

United Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta koma mataki na biyar a kan teburin Premier, bayan da ta yi nasarar cin West Ham United 2-1 a wasan mako na 34 da suka buga a Old Traford ranar Asabar.

United ta ci kwallayenta ta hannun Paul Pogba duk a bugun fenariti, ita kuwa West Ham ta ci nata kwallon ne ta hannun Felipe Anderson.

Da wannan sakamakon United ta koma ta koma ta biyar a kan teburin Premier da maki 64, Arsenal ta yi kasa zuwa mataki na shida da maki 63.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

United wadda ta yi rashin nasara a wasa biyu a Premier mai kwantan wasa daya, tana biye da Chelsea ta hudu mai maki 66, wadda za ta yi wasa ranar Lahadi da Liverpool.

United za ta ziyarci Barcelona a mako mai zuwa domin buga wasa na biyu da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.

A wasan farko da suka yi a Old Trafford, Barcelona ce ta yi nasara da ci daya mai ban haushi, bayan da United ta ci gida.

Labarai masu alaka