Afirka U-17: Najeriya ta doke Tanzania

Afirka Hakkin mallakar hoto The NFF

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta matasa 'yan kasa da shekara 17 ta yi nasara a kan mai masaukin baki Tanzaniya da ci 5-4 a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Wannan shi ne wasan farko da aka bude gasar ta matasa 'yan 17, domin fitar da wadan da za su wakilci Afirka a gasar kofin duniya.

Bayan da Najeria ta hada maki uku a rukunin farko, idan anjima ne Angola da Uganda za su kece raini a daya karawar rukunin farko.

A ranar Litinin rukuni na biyu zai fara wasa tsakanin Morocco da Senegal daga baya a kece-raini tsakanin Guinea da Kamaru.

Tawagar Najeriya wadda Manu Garba ke horas da ita, za ta yi wasa na biyu ranar Laraba da Angola.

Ita kuwa mai masaukin baki Tanzaniya wadda ta yi rashin nasara a wasan farko za ta yi wasa na biyu da Uganda a dai ranar ta Laraba.

Labarai masu alaka