Liverpool ta ci gaba da jan ragamar Premier

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images

Liverpool ta yi nasarar doke Chelsea da ci 2-0 a wasan mako na 34 a gasar cin kofin Premier da suka fafata a Anfield ranar Lahadi.

Liverpool ta ci kwallon farko ta hannun Sadio Mane tun kan je hutu, sannan Mohamed Salah ya ci na biyu minti takwas da komawa daga hutun da suka yi.

Da wannan sakamakon Liverpool tana nan a matakinta na daya a kan teburin Premier da maki 85, ita kuwa Manchester City wadda ta ci Crystal Palace tana ta biyu da maki 83.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Manchester City mai kwantan wasa daya ta doke Crystal Palace 3-1 a Selhust Park, kuma saura wasanta biyar ya rage a gasar Premier.

Sai dai City tana da wasa masu zafi da ya hada da karbar bakuncin Tottenham a gasar Premier da kuma zuwa gidan Manchester United.

Ita kuwa Liverpool ana ganin wasanninta hudu da suka rage mata ba su da zafi kamar na City, domin za ta fafata ne da Cardiff da Huddersfield da Newcastle da kuma Wolves.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Chelsea ta ci gaba da zama ta hudu a kan teburi, tana bin Tottenham mai kwantan wasa daya wadda ita ce ta uku.

Arsenal wadda take ta shida za ta iya maye gurbin Chelse a ranar Litinin da zarar ta yi nasara a kan Watford.

Liverpool ta taka rawar gani a Champions League

Chelsea ta tabuka a Europa League

Ko Man City za ta lashe kofi hudu kuwa?

Liverpool za ta ziyarci FC Porto a wasa na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions League, bayan da ta ci 2-0 a Anfield a karawar daf da na kusa da na karshe.

Daga nan ne Liverpool za ta ziyarci Cardiff City a wasan mako na 35 a gasar Premier ranar 21 ga watan Afirilu.

Jurgen Klopp ya ja ragamar Liverpool wasa na 200, shi ne wanda ya ci Chelsea.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea ma na buga gasar Zakarun Turai amma ta Europa, inda za ta karbi bakuncin Slavia Prague a wasan daf da na kusa da na karshe ranar Alhamis.

Sannan ta karbi bakuncin Burnley a gasar Premier karawar mako na 35 ranar 22 ga watan Afirilu.

Yadda kungiyoyin suka murza leda.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Labarai masu alaka