Real Madrid ta buga kunnen doki a Leganes

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Real Madrid ta tashi 1-1 da Leganes a wasan mako na 32 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata ranar Litinin.

Leganes ta fara cin kwallo ta hannun Jonathan Silva daf da za a je hutu, yayin da Madrid ta farke ta hannun Karim Benzema minti shida da komawa zagaye na biyu.

Wannan ne karo na hudu da Real ta yi canjaras, bayan cin wasa 19 aka doke ta tara, kuma saura karawa shida a kammala La Liga ta shekarar nan.

Real Madrid tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 61, ita kuwa Leganes maki 41 ne da ita, ita ce ta 11.

Barcelona ce ta daya da maki 74, sai Atletico Madrid ta biyu da maki 65, bayan buga wasannin mako na 32 a gasar ta La Liga.

Real Madrid ta ci karo da koma baya a kakar bana, bayan da aka fitar da ita a gasar Champions League da Copa del Rey.

'Yan wasan Real Madrid 19 da Zidane ya je da su Leganes.

Masu tsaron raga: Keylor Navas da Luca da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Vallejo da Varane da Nacho da Marcelo da kuma Odriozola.

Masu buga tsakiya: Modric da Casemiro da Valverde da M. Llorente da Asensio da Isco da kuma Ceballos.

Masu cin kwallo: Benzema da Bale da kuma Lucas Vázquez.

Labarai masu alaka