'Yan Man United 22 da suka je Barcelona

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan wasan Manchester United sun je Spaniya domin buga wasa na biyu da Barcelona na daf da na kusa da na karshe a Champions League.

A karawar farko da suka yi a Old Trafford a makon jiya, Barcelona ce ta yi nasara da ci 1-0, bayan da United ta ci gida.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tuni kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana 'yan wasa 22 da ya je da su Camp Nou ranar Litinin.

Cikin 'yan wasan da Red ta bayyana har da Matteo Darmian da Nemanja Matic da kuma Alexis Sanchez wadan da suke yin jiya.

United ta koma ta biyar a teburin Premier

'Yan Man United nawa ne ke jinya

Ronaldo ya ci kwallo 125 a Champions League

Luke Shaw yana daga cikin 'yan wasan da United ta je da su Spaniya, duk da cewar an dakatar da shi wasa daya, bayan da aka ba shi katin gargadi a karawa da Barcelona a Ingila.

A ranar Asabar ne United ta ci West Ham United 2-1 a wasan mako na 34 a gasar cin kofin Premier da suka fafata a Old Trafford.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

'Yan wasan Manchester United

Masu tsaron raga: David De Gea da Sergio Romero da Lee Grant

Masu tsaron baya: Diogo Dalot da Matteo Darmian da Ashley Young da Phil Jones da Victor Lindelof da Marcos Rojo da Chris Smalling da kuma Luke Shaw.

Masu wasan tsakiya: Fred da Nemanja Matic da Scott McTominay da Andreas Pereira da Paul Pogba da Jesse Lingard da Juan Mata

Masu cin kwallo: Anthony Martial da Alexis Sanchez da Romelu Lukaku da Marcus Rashford.

Labarai masu alaka