Aubameyang ya kai Arsenal ta hudu a Premier

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal ta yi nasarar doke Watford da ci 1-0 a wasan mako na 34 a gasar cin kofin Premier da suka fafata ranar Litinin.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya ci wa Arsenal kwallon minti 10 da fara tamaula, kuma minti daya tsakani aka bai wa kyaftin din Watford Troy Deeney jan kati.

An kori Deeney daga fili ne, bayan da ya yi wa Lucas Torreira keta, kuma karon farko da ya karbi jan kati tun Disambar 2017.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta hudu a kan teburi da maki 66, Chelsea ma maki 66 ne da ita tana ta biyar, sai Manchester United ta shida mai maki 64.

Yadda kungiyoyin biyu suka murza leda

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Labarai masu alaka