'Yan Barca da United da suka fafata a Camp Nou

Barca United Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Talata Barcelona za ta karbi bakuncin Manchester United a wasa na biyu na daf da kusa da karshe a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

A wasan farko da suka buga a Old Trafford a makon jiya, Barcelona ce ta yi nasara da ci 1-0.

Tuni kocin Barcelona ya bayyana 'yan wasa 18 domin fuskantar Manchester United a Camp Nou.

'Yan wasan Barcelona:

Ter Stegen da Semedo da Piqué da Rakitic da Sergio da Coutinho da Arthur da Suárez da kuma Lionel Messi.

Sauran sun hada da Dembélé da Cillessen da Malcom da Lenglet da Jordi Alba da Roberto da Vidal da Umtiti da kuma Alena.

'Yan wasan Manchester United

Masu tsaron raga: David De Gea da Sergio Romero da Lee Grant

Masu tsaron baya: Diogo Dalot da Matteo Darmian da Ashley Young da Phil Jones da Victor Lindelof da Marcos Rojo da Chris Smalling da kuma Luke Shaw.

Masu wasan tsakiya: Fred da Nemanja Matic da Scott McTominay da Andreas Pereira da Paul Pogba da Jesse Lingard da Juan Mata

Masu cin kwallo: Anthony Martial da Alexis Sanchez da Romelu Lukaku da Marcus Rashford.