Afirka U-17: Najeriya ta ci wasa na biyu

Asalin hoton, The NFF
Tawagar kwallon kafar Najeriya ta matasa 'yan kasa da shekara 17 ta kai wasan zagaye na biyu a gasar nahiyar Afirka ta matasa da ake yi a Tanzania.
Golden Eaglets ta yi nasarar doke Angola 1-0 a karawar da suka yi ranar Laraba, kuma Olakunle Olusegun ne ya ci kwallon a bugun fenariti minti 20 da fara tamaula.
Da wannan sakamakon Najeriya ta hada maki shida ita ce kan gaba a rukunin farko, bayan da ta ci mai masukin baki Tanzaniya 5-4 a wasan farko na cikin rukuni.
Angola wadda ta ci Uganda 1-0 a wasan farko tana ta biyu da maki uku, sai anjima ne Tanzania da Uganda za su kece-raini.
Sai a ranar ta Alhamis rukuni na biyu zai yi wasa na biyu, inda za a kara tsakanin Guinea da Senegal da fafatawa tsakanin Kamaru da Morocco.
Kamaru tana da maki uku, bayan da ta doke Guine 2-0 a wasan farko, su kuwa Senegal da Morocco 1-1 suka yi.