Zakarun Turai: Ranar wasan Liverpool da Tottenham

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA ta bayyana ranar da Liverpool da Tottenham za su buga wasanninsu na daf da karshe a Champions League.

Tottenham za ta karbi bakuncin Ajax ranar Talata 30 ga watan Afirilu, sannan su buga wasa na biyu ranar Laraba, 8 ga watan Mayu a Amsterdam.

Ita kuwa Liverpool za ta fara ziyartar Barcelona ranar Laraba 1 ga watan Mayu, sannan su kara a wasa na biyu a Anfield ranar Talata, 7 ga watan Mayu.

Hakan na nufin mahukuntan gasar Premier sai sun sauya ranakun da Tottenham da Liverpool za su fafata ganin ya ci karo da gasar ta Zakarun Turai.

An tsara cewar Liverpool za ta kara da Newcastle United ranar Lahadi 7 ga watan Mayu, kwana biyu da za ta karbi bakuncin Barcelona a Anfield.

Ita kuwa Tottenham za ta kara da Bournemouth ranar Litinin 6 ga watan Mayu, ita ma kwana biyu ta fafata da Ajax a Amsterdam a wasan daf da karshe a Champions League.

Asalin hoton, BBC Sport

Tottenham ta yi nasarar fitar da Manchester City, bayan da ta ci 1-0 a gidanta, sannan suka tashi 4-3 a Etihad ranar Laraba, jumulla 4-4.

Ita kuwa Liverpool ta yi nasara ne a kan Porto, bayan da ta ci 2-0 a Anfield, sannan ta zura kwallo 4-1 a Portugal.

Liverpool tana mataki na daya a teburin Premier da maki 85, ita kuwa Tottenham tana ta uku da maki 67.

A ranar Asabar ne Manchester City za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan mako na 35 a gasar Premier, ita kuwa Liverpool za ta je Cardiff City.

Asalin hoton, BBC Sport