Ku kada kuri'arku ga gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC ta 2019

Lucy Bronze
Bayanan hoto,

Lucy Bronze ta Ingila ita ce ke rike da kambin a yanzu

An fitar da jerin sunayen 'yan takarar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC ta 2019, saboda haka za ku iya zabar wadda kuke so.

Kwararru ne wadanda suka hada da masu horad da 'yan wasa da 'yan wasa da jami'ai da kuma 'yan jarida suka tace sannan suka zabo 'yan wasa biyar domin samun kyautar gwarzuwar 'yar kwallon kafar ta duniya ta BBC ta 2019.

Wadanda aka zabo su ne:

  • Pernille Harder - 'Yar gaban Vfl Wolfsburg
  • Ada Hegerberg - 'Yar gaban Olympique Lyonnais
  • Lindsey Horan - 'Yar wasan tsakiyar Portland Thorns
  • Sam Kerr - 'Yar gaban Chicago Red Stars and Perth Glory
  • Saki Kumagai - 'Yar bayan Olympique Lyonnais

Za a rufe kada kuri'a a ranar Alhamis, 2 ga Mayu da karfe 8:00 na safe agogon GMT, 9:00 na safe agogon Najeriya da Nijar kenan, sannan za a bayyana wadda ta yi nasara ranar Laraba, 22 ga watan Mayu a tashar BBC da ke watsa shirye-shiryenta ga duniya da kuma shafin wasanni na intanet na BBC.

Za ku iya latsa nan domin kada kuri'arku click here to vote.

Ga karin bayani game da 'yan wasa biyar din da aka zaba domin fitar da gwanar da za ta samu kyautar wadda ke cikin shekara ta biyar.

Pernille Harder

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Pernille Harder

Shekara: 26 Kasarta: Denmark Wasannin da ta yi wa kasarta: 110

Kungiyarta: VFL Wolfsburg Inda take wasa a fili: Gaba

Harder ta kammala kakar 2017-18 a matsayin wadda ta fi kowa yawan cin kwallo a gasar Bundesliga ta Jamus, ta mata inda ta jefa kwallo 17, kuma ta taimaka wa kungiyar Wolfsburg ta dauki kofin gasar sau biyu a jere.

Haka kuma ta yi wasa kuma ta ci a wasanta na farko na gasar Zakarun Turai, a karawar karshe ta shekarar da ta wuce a fafatawar da suka yi da Olympique Lyonnais, amma kuma ba su dauki kofi ba, saboda sun sha kashi da ci 4-1 a gidan 'yan Faransan.

Amma kuma duk da haka Harder ta samu kyautar zama gwarzuwar 'yar wasa ta Uefa ta shekarar 2018. Haka kuma ta zamo ta biyu a gasar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta duniya ta mata, wato Ballon d'Or.

Ada Hegerberg

Asalin hoton, RONNY HARTMANN

Bayanan hoto,

Ada Hegerberg

Shekara: 23 Kasa: Norway Wasannin da ta yi wa kasarta: 66

Kungiya: Olympique Lyonnais Inda take wasa a fili: Gaba

Hegerberg ta ci kofinta na Zakarun Turai na uku a jere da kungiyar Olympique Lyonnais, a shekarar da ta wuce, inda ta kafa tarihin cin kwallo 15 a gasar, kuma kungiyarta ta dauki kofin gasar Faransa da kuma kofin Zakarun Turai duka biyu.

Hegerberg ta ci wa kungiyarta kwallo 193, tun lokacin da ta koma a 2014, inda ta ci 19 daga ciki a wasannin gasar lig din kasar guda 18 a kakar nan. A bazarar da ta wuce ne ta kulla doguwar yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar.

'Yar wasan ta Norway, wadda ta daina buga wa kasarta, ita ce ta farko da ta taba cin kyautar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta duniya ta mata, Ballon d'Or a 2018.

Lindsey Horan

Asalin hoton, MARK RALSTON

Bayanan hoto,

Lindsey Horan

Shekara: 24 Kasa: Amurka Yawan wasan da ta yi wa kasarta: 62

Kungiya: Portland Thorns Wurin wasanta fili: Tsakiya

A watan Satumba na 2018, an bayyana Horan a matsayin 'yar wasa mafi daraja ta gasar kwallon kafa ta mata ta Amurka (NWSL).

Ta zama 'yar wasan kungiyar Portland Thorns ta farko da ta samu wannan kyauta bayan da ta ci kwallo 13 , kuma ta bayar aka ci biyu a wasa 22 da ta yi a kakar.

Horan ta taimaka wa kungiyarta ta kai wasan karshe na gasar mata ta Amurka NWSL Championship, inda suka zamo na biyu a tebur, a bayan North Carolina Courage ta daya.

Sam Kerr

Asalin hoton, DANIEL POCKETT

Bayanan hoto,

Sam Kerr

Shekara: 25 Kasa: Australia Yawan wasan da ta yi wa kasarta: 67

Kungiya: Perth Glory da Chicago Red Stars Inda take wasa a fili: Gaba

Yanzu tana yin wasa a kungiyoyi biyu na Perth Glory da Chicago Red Stars. Kerr ita ce ta fi kowace 'yar wasa cin yawan kwallo a tarihin gasar kwallon mata ta Amurka ta NWSL, kuma watan Janairu na wannan shekarar ta 2019 ta kafa irin wannan tarihi a gasar Australiya ta W League.

Ta ci kyautar wadda ta fi yawan zura kwallo a raga karo na biyu a jere a gasar kwallon kafar ta mata ta Amurka a 2018, inda ta kammala gasar da yawan kwallo 16, ta kuma taimaka aka ci hudu a wasa 19 a kungiyar Red Stars.

An nada Kerr a matsayin kyaftin din tawagar 'yan wasan kasar Australia a watan Fabrairu, kuma ta jagorance su zuwa gasar cin kofin kasashe a karon farko.

Saki Kumagai

Asalin hoton, FRANCK FIFE

Bayanan hoto,

Saki Kumagai

Shekara: 28 Kasa: Japan Yawan wasan da ta yi wa kasarta: 102

Kungiya: Olympique Lyonnais Inda take wasa a fili: 'Yar baya/Mai tsaro a tsakiya

Ta dauki Kofin Duniya da Japan, sannan kuma ta jagoranci tawagar kasar tata a matsayin kyaftin zuwa gasar cin kofin kasashen Asia a 2018 - inda a karon farko suka ci wasa a gasar a cikin shekara hudu.

Haka kuma tana cikin tawagar 'yan wasan kungiyar Olympique Lyonnais da ta dauki kofi biyu a kakar 2017-18. Sannan kuma ta dauki kofin Zakarun Turai uku.

Kumagai ta taka rawa a bajintar da kungiyar ta Faransa ta yi ta kafa tarihin hana zura mata kwallo da yawa a gasar lig ta Faransa, inda aka jefa musu kwallo shida kawai a wasa 20.