Mohamed Salah ya shiga jerin mutum 100 mafiya tasiri a duniya

Singer Taylor Swift, actor Dwayne 'The Rock' Johnson, actor Sandra Oh, TV news presenter Gayle King, US politician Nancy Pelosi and Liverpool striker Mohamed Salah

Asalin hoton, Time

Bayanan hoto,

Daga hagu zuwa dama: Taylor Swift da Dwayne 'The Rock' Johnson da Sandra Oh da Mohamed Salah, da Nancy Pelosi da kuma Gayle King

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya bukaci da a rika martaba mata musamman a yankin Gabas ta Tsakiya yayin da mujallar Time ta sanya shi a cikin jerin mutum 100 mafiya tasiri a duniya.

Dan kwallon gaban mai shekara 26 yana cikin muhimman mutane shida da mujallar Amurkan ta yi bangonta da su.

"Muna bukatar sauyi kan yadda muke kula da mata a al'adarmu," kamar yadda ya shaida wa mujallar Time.

"Wannan ya dace a rika yi, ba zabi ba ne."

Ya ci gaba da cewa "Ina taimakon mata fiye da yadda nake yi a baya, saboda ina ganin sun cancanci fiye da abin da suke samu a yanzu."

Salah ya shiga jerin mutane kamar shahararriyar mawakiyar nan Lady Gaga da Shugaban Amurka Donald Trump da Firai Ministan Pakistan kuma tsohon dan wasan Cricket Imran Khan da Mai Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg da Uwar gidan tsohon Shugaba Obama.

Dan kwallon ya koma Liverpool ne daga Roma a shekarar 2017 kuma ya ci kwallaye 44 a kakarsa ta farko a kungiyar.

A kakar bana, ya ci wa Liverpool kwallaye 19 a gasar Firimiyar bana, wanda kungiyar ce take saman teburin gasar a halin yanzu.

A wasan da aka buga a daren jiya Laraba na gasar Zakarun Turai, wanda Liverpool ta doke FC Porto da 4-1 Mohamed Salah ne ya zura kwallo ta biyu a minti 65.

Bajintar da dan wasan ya nuna a kakar bara ta 2017-2018 ta sa duk duniya ta karkato kansa, inda aka yi ta magana a kansa kamar ba gobe.

Sunan Salah ya fito har a takardar tambayar jarrabawar daliban Shari'a na jami'ar Damascus, inda ake tambayarsu game da ketar da Sagio Ramos ya yi wa Salah a fafatawar da suka yi a wasan karshe na gasar Zakarun Turai ta shekarar 2017-2018.

An tambayi daliban da su fadi dalilan da ya sa ba za a iya kama Ramos da laifi ba a bisa tsarin shari'a.