Afirka U-17: Kamaru ta kai kofin duniya

U17

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Kamaru ta matasa 'yan kasa da shekara 17 ta yi nasarar doke ta Morocco da ci 2-1 a gasar nahiyar Afirka da ake yi a Tanzania.

Tun farko sai da aka fara cin Kamaru daga baya ne ta farke, sannan ta kara kwallo na biyu.

Wannan shi ne wasa na biyu da Kamru ta yi nasara a gasar, wanda hakan ya kai ta karawar daf da karshe.

A ranar Litinin kasar ta yi nasarar cin Guinea 2-0 a wasan farko na rukuni na biyu, daya wasan na rukuni na biyu, Guinea ce ta doke Senegal 2-1.

Duk kasashen da suka kai wasan daf da karshe, sune za su wakilci Afirka a gasar kwallon kafa ta matasa da za a yi a Brazil a bana.

Tawagar matasan Najeriya ma ta kai zagayen daf da karshe, bayan da ta doke mai masaukin baki Tanzaniya 5-4 ranar Litinin, sannan ta ci Angola 1-0 ranar Laraba.

A ranar Asabar za a karkare wasannin rukunin farko, inda za a kece-raini tsakanin Najeria da Uganda da fafatawa tsakanin mai masaukin baki Tanzania da Angola.

Shi kuwa rukuni na biyu zai karkare wasanninsa ranar Lahadi tsakanin Kamaru da Senegal da fafatawa tsakanin Guinea da Morocco.