'Yan takarar gwarzon kungiyar masu buga Premier

Premier

Asalin hoton, Getty Images

'Yan Manchester City uku na cikin shidan da aka bayyana don fitar da gwarzon kungiyar kwararrun 'yan kwallon da ke buga Premier na bana.

Cikin 'yan kwallon City har da Bernardo Silva da Raheem Sterling da kuma Sergio Aguero da aka bayyana daga kungiyar da ta lashe Premier bara.

Ita kuwa Liverpool tana dauke da 'yan kwallo biyu da suka hada da Virgil van Dijk da kuma Sadio Mane.

Dan wasan Chelsea, Eden Hazard shi ne cikon na shida da za a zabi daya daga cikin su, domin karrama gwanin bana na PFA.

Mohammed Salah na Liverpool ne ya lashe kyautar bara ta 2017-18, inda Sterling ya zama matashin da yafi taka rawa a kungiyar ta PFA, wanda ya lashe kyautar a 2018.

Cikin wadanda ya yi takara da su har da abokin wasansa a Manchester City, Silva.

Bayan Sterling din akwai 'yan Ingila uku da ke takarar gwarzon matashin dan wasa na kungiyar na bana da suka hada da Marcus Rashford na Manchester United mai shekara 21 da Trent Alexander-Arnold mai shekara 21 dan kwallon Liverpool.

Na ukun shi ne mai shekara 20 mai taka leda a West Ham United, Declan Rice, haka kuma da dan wasan Bournemouth mai shekara 21, David Brooks daga shidan da za a fitar da gwani.

Dan wasan sai yana kasa da shekara 23 mai buga gasar Premier shi ne zai cancanci shiga gasar matashin da yafi kwazo da kungiyar kwararrun 'yan wasan Premier za su zaba.

Za kuma a bayyana zakaru ranar 28 ga watan Afirilu a London Grosvenor House.

Wadanda ke yin takara

Asalin hoton, BBC Sport

Dan wasan Manchester City da tawagar kwallon kafar Ingila Sterling na taka rawa a kakar bana, inda tuni ya ci kwallo 23 a dukkan wasannin da ya buga.

Dan wasan mai shekara 24 yana daga kashin bayan da ke jan ragamar City wajen kokarin lashe kofi uku a bana, tarihin da kungiyar ke son yi a karon farko a tarihi.

Shin ko kasan Sterling ya ci kwallo 23 ya taimaka aka zura 13 a raga a wasa 45 da ya yi a bana?

Asalin hoton, BBC Sport

Dan wasan tawagar Argentina ya bayar da gudunmawar da ke daf da kai Manchester City lashe kofin Premierna bana kuma na hudu jumulla.

Dan wasan mai shekara 30, yana cikin 'yan wasa 11 na PFA a shekara 2017-18, ya kuma ci kwallo 30 a dukkan karawa kuma karo na biyar a kaka takwas da ya yi a Etihad.

Aguero na takarar lashe takalmin zinare na gasar Premier tare da Mohamed Salah na Liverpool duk da cewar baya buga wasa da yawa kamar yadda dan kasar Masar ke yi.

Ko kasan cewar kwallo 30 da Aguero ya ci a dukkan wasannin bana, shi ne ke kan gaba tsakanin masu buga Premier a kakar bana, ya taimaka aka ci tara a wasa 41 da ya buga.

Asalin hoton, BBC Sport

Tsabar kudin da Liverpool ta kashe na fam miliyan 75 kan sayo Virgil van Dijk a Janairun 2018 ya taimaka mata wajen takarar lashe kofin Premier na bana.

Dan wasan mai shekara 27 dan kwallon tawagar Netherlands ya taimakawa Liverpool da yin wasa 17 daga 34 ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, kuma 15 aka ci Liverpool a bana.

Ko kasan cewar kokarin da Virgil van Dijk ke sawa ana samun nasara ya kai kaso 77 cikin 100 a masu tsaron baya a Premier shekarar nan?

Virgil van Dijk ya buga wasa 43 ba a zura wa Liverpool kwallo a raga a wasa 22, shi kuma ya ci 5 a Premier.

Asalin hoton, BBC Sport

Dan wasan tawagar Senegal Mane yana cikin wadanda suka yi takarar kyautar 2016-17, kuma tun daga lokacin kokarin dan kwallon mai shekara 27 ke kara karuwa.

Ya kan rikirkita masu tsaron baya cikin 'yan gaban Liverpool da suka hada da Salah da Roberto Firmino, kuma Salah ya ci kwallo 18 a Premier bana.

Haka kuma kwallo 22 da ya ci wa Liverpool a dukkan karawa a bana, shi ne kwazon da ya yi mafi kyau tun sayen sa da Southampton ta yi daga Red Bull Salzburg a 2014.

Ko kasan cewar Steven Gerarrad ne ya ci wa Liverpool kwallo 21 a gasar European Cup ko kuma Champions League fiye da Mane mai 14?

Mane ya yi wasa 43 a bana ya ci kwallo 22 ya kuma taimaka aka zura biyar a raga.

Asalin hoton, BBC Sport

Idan har Kevin de Bruyne bai buga wa Manchester City wasa ba, dan kwallon tawagar Portugal Bernardo Silva na nuna kanshi a matsayin gwanin buga tsakiya.

A kaka ta biyu da da yake a Etihad tun sayo shi da aka yi daga Monaco kan fam miliyan 43 a 2017, Silva ya buga manya wasa 31.

Ko kasan cewar Silva ya ci kwallo 12 ya taimaka aka zura 11 a karawa 53 tun daga bara?

Asalin hoton, BBC Sport

Tun lokacin da ake ta cece-kuce kan barin Chelsea da zai yi, Hazard wanda ya taimakawa Belgium ta kai wasan daf da karshe a kofin duniya a Rasha a 2018, dan wasan ke kara kokari a Blues.

Kocin Maurizio Sarri wanda ke kokarin rike dan wasan ko ta halin kaka, ya ce Hazard mai shekara 27 zai zama fitatce a fagen tamaula a duniya.

Hazard ya shiga 'yan wasa 11 na PFA karo hudu a kaka biyar baya, kuma har yanzu shi ne kashin bayan Chelsea a wasannin da take yi.

Ko kasan cewar Hazard ya ci kwallo 16 ya kuma taimaka aka zura 12 a raga a karawa 44 da ya yi a bana?