Me ke hana 'yan wasan Najeriya dadewa suna haskawa?

Taye Taiwo da Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

  • Wannan makala ce da wani mai sharhi kan harkokin wasanni a Najeriya Isiyaku Muhammad Ango ya rubuta mana.

A duk lokacin da ake batun 'yan wasan kwallon kafa a duniya, zai yi wuya a shafa fatiha ba tare da an kira Najeriya ba saboda yadda kasar ke fitar da zaratan 'yan wasa da suke tasiri a duniya.

'Yan wasan Najeriya da dama sukan fito da karfinsu, amma abin mamaki cikin kankanin lokaci sai ka neme su ka rasa, abin kamar almara.

Idan an je gasar cin kofin 'yan kasa da shekara 17 da 20, har kasar Brazil da ake ganin ta shahara a kwallon kafa, ta kan yi fargaba haduwa da Najeriya.

Misali a gasar cin Kofin Duniya na 'yan kasa da shekara 17 wato U-17, Najeriya ta fi kowace kasa lashe gasar, inda ta ci kofin sau biyar a shekarun 1985 da 1993 da 2007 da 2013 da 2015, sannan kuma ta zo na biyu a shekarun 1987 da 2001 da 2009.

Sai kasar Brazil wadda ta lashe gasar sau uku.

Kuma Najeriya ta kan samu kyaututtuka kamar ta dan wasan da ya fi zura kwallaye (Golden Boot) da sauransu.

Haka gasar 'yan kasa da shekara 20 wanda duk da ba ta taba lashewa ba, Najeriya ta zo ta biyu sau biyu a shekarun 1989 da 2005.

Amma yawancin lokuta, 'yan wasan kasashen wajen sai tauraronsu ya ci gaba da haskawa, amma 'yan Najeriya kuma ta su ta rika dusashewa.

Misalan 'yan wasan Najeriya da takwarorinsu na kasashen waje da suka taso tare:

1. Crisantus Macauley da Toni Kroos da Eden Hazard da David De Gea

A gasar cin Kofin Duniya ta 'yan kasa da shekara 17 a shekarar 2007 da aka buga a kasar Koriya ta Kudu.

Najeriya ce ta lashe gasar, sannan kuma dan kasar Crisantus Macauley ne ya fi zuwa kwallaye (Golden Boot), sannan kuma ya zo na biyu a wadanda suka fi iya taka leda (Silver Ball) bayan Toni Kross (Golden Ball) sannan Bojan Krkic na uku wanda yanzu yake Stoke City a Ingila.

Asalin hoton, Getty Images

Yanzu haka Crisantus yana kulob din UB Conquense da ke rukunin Tercera na Spain.

Tercera ne rukuni na hudu a Spain bayan Laliga da Segunda da Segunda B.

Amma Kroos yanzu haka ana iya cewa ya ci komai a duniyar kwallo kamar Gasar Zakarun Turai sau hudu da Kofin Duniya da La liga da Bundesliga sau uku da sauransu.

Sauran 'yan wasan gasar akwai Bojan da Daniel Welbeck da Victor Moses (lokacin yana wakiltar Ingila) da Cristian Benteke da Nacho.

Amma duk da wadannan 'yan wasan, Crisantus ne ya lashe kyautar Golden Ball da Silver Boot.

2. Mikel Obi da Taye Taiwo da Lionel Messi

Asalin hoton, Facebook

A gasar cin Kofin Duniya na 'yan kasa da shekara 20 ta shekarar 2005 a Holland lokacin ana kiran gasar World Youth Championship, inda Ajantina ta lallasa Najeriya da ci biyu da nema a wasan karshe.

Mikel Obi ne na biyu a cikin wadanda suka fi taka leda a gasar (Silver Boot) bayan Messi da ya zo na daya (Golden Boot).

Yanzu Mikel yana kungiyar Middlesbrough ne ta rukuni na biyu a Ingila, shi kuma Messi abin ba a cewa komai.

Sai kuma Taye Taiwo, wanda shi kuma yanzu haka yake rara-gefe a kasar Finland a kungiyar RoPS.

Sauran 'yan wasan da suka buga gasar sun hada da Fagregas da Aguero da sauransu.

3. Sani Emmaneul, Abdul Ajagun, Neymar Jnr, Isco, da Morata

A gasar Kofin Duniya ta 2009 a Najeriya inda kasar Switzerland ta doke Najeriya a bugun karshe.

Dan wasan Najeriya Sani Emmanuel ne ya lashe kyautar wanda ya fi taka leda (Golden Boot).

Asalin hoton, Getty Images

Amma tun a shekarar 2015 da ya bar Oskarshamn a Sweden, har yanzu yana zaman kashe wando ne.

Shi kuma Ajagun, wanda a lokacin shi ne kyaftin yana kungiyar Omonia Nikosia a kasar Cyprus a matsayin aro daga KV Kortrijk ta Holland.

Sauran 'yan wasan gasar sun hada da Marc-Andre ter Stegen - wato golan Barcelona, da Mario Gotze da Kenneth Omeruo na Najeriya da Coutinho da Casemiro da sauransu.

Amma duk da wadannan 'yan wasan, dan Najeriya ne ya lashe kyautar Golden Boot.

Sauran 'yan wasa da suka taso amma suka yi kasa daga baya akwai Kellechi Iheanacho (Leicester City) da Musa Yahaya (FC Porto B) da sauransu.

Dalilin da tauraronsu ke dusashewa da sauri

Akwai abubuwa da suke taimakawa wajen dusashen haske da tauraron 'yan wasan Najeriya cikin sauri. Amma manyan abubuwan sun hada da:

1. Talauci.

Da yawa daga cikin masu kallon kwallo za su yi mamaki ganin talauci a matsayin abin da ke jawo wa 'yan wasan Najeriya durkushewa cikin sauri.

A lokuta da yawa 'yan wasan Najeriya suna buga kwallo ne kawai saboda rashin sana'a, ko kuma idan wani makwabci ko abokinsu ya tsallaka ya dawo da kudade, kasancewar wasu 'yan kasar suna son yin kudi cikin sauri.

Daga nan, sai suka dauki hanyar a matsayin hanyar samun kudi cikin sauri.

Wannan ya sa da yawa daga cikinsu ba su da kauna da shaukin kwallon, kawai kudin suke bukata.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Da sun buga wa Najeriya burinsu su samu kulob da zai dauke su, ya biya su makudan kudi.

Galibinsu da sun ga wasu kudade makare a asusun ajiyansu, sai su ji kawai sun wuce wajen.

Daga nan, sai su daina dagewa da ci gaba da zage damtsensu.

Hakan yakan cire musu ci gaba da gogayya da takwarorinsu, wanda kuma kwallo idan aka cire gasar, ita kanta ta mutu.

2. Zargin magudin shekaru

Akwai zargin da aka dade ana yi wato batun cewa yawancin 'yan wasan Najeriya suna zuwa gasar 'yan kasa da shekara 17 a lokacin da shekarunsu ya wuce hakan.

Sai dai wasu suna ganin ba wai kawai a Najeriya ake samun irin wannan matsala ba.

Wasu na ganin, za a iya samun dan shekara 25 daga nahiyar Afirka wanda zai je gasar kasa da shekara 17, don haka bayan shekara biyar, ya zama shekara 30 ke nan a zahiri, amma kuma shekarunsa 22 na kwallo.

Wannan yake sa shakaru su rinjaye shi, kawai sai ka ga kamar an kwashe masa iya kwallon.

Kodayake, hukumomin da ke kula da harkokin kwalloon kafa a kasashen Afirka suna musunta wannan zargi.

3. Siyasa

Har ila yau, akwai wadanda suke ganin siyasa ma tana taka muhimmiyar rawa wajen hana 'yan wasa haskawa.

Akwai masu zargin cewa ana samun lokutan da ake sanya son zuciya wajen daukan 'yan wasan, "inda sai wanda ya san wani ake dauka."

Koda kuwa mutum shekarunsa sun wuce, idan yana da uwa a bakin murhu za a iya daukarsa, sai a zubar da wadanda ya kamata a dauka.